(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya bayyana a safiwa yau Asabar kan cewa za’a gudanar da bincike don gano wadanda suka yi kuskuren kakkabo jirgin saman fasinjar kasar Ukrai wanda ya yi hatsarin jim kadan bayan tashinsa daga tashar jiragen sama na Imam Khumaini International Airport a nan Tehran a ranar Laraban da ta gabata.
Shugaban ya bayana takaicinsa da wannan kuskuren ya kuma mika ta’aziyarsa ga wadanda abin ya shafa musamman yan uwan fasinjojin jirgin da ma’aikata da suka rasa rayukansu.
A halin yanzu dai gwamnatin Ukrai ta ce an mika mata bakin akwatin jirgin don tabbatar da abinda ya jawo hatsarin jirgin, sannan jami’an gwamnatin kasar Iran suna bada hadin kai da ya dace don kaiwa ga hakan. Dukkan mutane 176 da suka cikin jirgin sun rasa rayukansu.
/129